logo

HAUSA

Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kudurin kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a zirin Gaza

2024-06-11 11:46:28 CMG Hausa

 

Kwamitin sulhu na MDD ya zartas da kuduri mai lamba 2735 a jiya Litinin, inda ya yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a zirin Gaza nan da nan a duk fannoni, ta yadda za a kawo karshen rikicin da ya dabaibaye wurin tsawon watanni 8.

14 daga mambobi 15 na kwamitin, sun kada kuri’ar amincewa da kudurin, yayin da Rasha ta kada kuri’ar janye jiki.

Kudurin ya gabatar da shawarwarin shawo kan rikici a Gaza cikin kashi 3. Ya kuma nanata cewa, kwamitin bai yarda da duk wani yunkuri na canja filaye ko yawan jama’ar yankin ba, tare da nanata niyyarsa ta nacewa ga alkawarin tabbatar da “Kafa kasashen Palasdinu da Isra’ila”.

Fadar shugaban Palasdinu ta gabatar da sanarwa a wannan rana cewa, wannan kuduri wani mataki ne mai yakini da aka samu wajen warware rikicin.

A wannan rana kuma, kungiyar Hamas ta ba da sanarwar amincewa da kudurin, tare da bayyana burin hawan teburin sulhu, da halartar shawarwarin da suka dace da fatan al’ummar zirin Gaza da Hamas a fakaice. (Amina Xu)