Abdulrahman Chukkol: Yadda Sinawa ke himmatuwa wajen aiki ya burge ni sosai!
2024-06-11 15:49:44 CMG Hausa
Abdulrahman Chukkol, dan asalin birnin Yola ne dake jihar Adamawa a tarayyar Najeriya, wanda a yanzu haka yake karatun digiri na uku a wata jami’a mai suna BIT dake nan birnin Beijing na kasar Sin.
A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, malam Abdulrahman Chukkol wanda ya shigo kasar Sin tun shekara ta 2019, ya bayyana yadda rayuwa da karatunsa yake a birnin Beijing, kuma a cewarsa, akwai abubuwa da dama da suka burge shi a nan kasar Sin, musammam yadda kasar take da tsaro da kwanciyar hankali, da kuma yadda al’ummar kasar ke nuna himma da kwazo wajen aiki.
A karshe, malam Abdulrahman Chukkol ya yi kira ga matasan Najeriya, da su tashi su yi aiki don samun nasara. (Murtala Zhang)