logo

HAUSA

Li Qiang zai kai ziyarar aiki a New Zealand da Austriliya da Malaysia

2024-06-11 16:37:33 CMG Hausa

 Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Lin Jian ya sanar a yau Talata cewa, firaministan kasar Sin Li Qiang, zai kai ziyarar aiki a kasashen New Zealand da Austriliya da Malaysia, daga ran 13 zuwa 20 ga wannan wata, bisa gayyatar da takwarorinsa na wadannan kasashe suka yi masa. Yayin ziyararsa a Austriliya, Li Qiang zai halarci taron shekara-shekara na firaministocin kasashen Sin da Austriliya karo na 9 da takwaransa na kasar.(Amina Xu)