logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwaransa ta Afirka ta kudu

2024-06-11 19:40:49 CMG Hausa

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da takwaransa ta Afirka ta kudu Naledi Pandor, a garin Nizhni Novgorod na kasar Russia.

Yayin zantawar ta su a jiya Talata, Wang Yi ya taya Afirka ta kudu murnar gudanar da babban zaben kasa cikin nasara, yana mai bayyana yadda Sin ke dora muhimmancin gaske ga ci gaban Afirka ta kudu, a matsayin ta na babbar kasa mai tasowa. Ya ce Sin a shirye take ta yi aiki tukuru tare da sassan kasa da kasa a fannin tsare tsare, da samar da murya mai ma’ana, kuma mai daidaito, game da muhimman batutuwa dake addabar duniya, kamar rikicin Ukraine, kana tana fatan ba da gudummawa ga wanzar da zaman lafiya da daidaito a duniya.

A nata bangare kuwa, Naledi Pandor, cewa ta yi Afirka ta kudu na jinjinawa kokarin kasar Sin, na ganin an warware rikicin Ukraine ta hanyar siyasa, da yayata bukatar dakatar da bude wuta a Gaza. Ya ce Afirka ta kudu a shirye take ta karfafa hadin gwiwa da Sin, karkashin dandalolin kasa da kasa, irin su kungiyar BRICS, da G20, don tabbatar da an cimma nasarar raya ci gaban tsare tsaren da ake gudanarwa karkashin su yadda ya kamata. (Saminu Alhassam)