Mataimakin ministan harkokin wajen Sin: Ana kokarin tabbatar da zaman lafiya da hadin gwiwa a nahiyar Asiya
2024-06-10 15:16:17 CMG Hausa
A kwanan baya, Sun Weidong, mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, ya jagoranci tawagar kasar wajen halartar taron manyan jami'ai na kungiyar kasashen dake gabashi da kudancin nahiyar Asiya (ASEAN) da kasashen Sin, da Japan, da Koriya ta Kudu, gami da sauran taruka na gabashin Asiya da na kungiyar ASEAN, da suka gudana a kasar Laos. Inda jami'in na kasar Sin ya gaya ma manema labaru cewa, kasashe mahalarta tarukan sun yi musayar ra'ayoyi mai zurfi, tare da cimma matsaya kan dimbin ayyuka daban daban.
A cewar Mista Sun Weidong, babban dalilin da ya haifar da kalubale ga tsaron yankin teku dake kudancin kasar Sin, shi ne aikace-aikacen ta da rikici da rurura wuta, da kasar Amurka, gami da sauran bangarorin dake wajen yankin suke yi. Jami'in ya nanata cikakken ikon da kasar Sin ke da shi na mallakar dimbin tsibiran dake cikin yankin tekun kudancin Sin, da niyyar kasar ta daidaita bambancin ra'ayi da sauran kasashe, ta hanyar shawarwari.
Jami'in na kasar Sin ya kara da cewa, kasashen Asiya mahalarta tarukan da suka gudana a kasar Laos, sun jaddada bukatar tabbatar da zaman lafiya, da hadin kai, da neman samun ci gaban tattalin arziki na bai daya, a nahiyar da suke ciki. (Bello Wang)