logo

HAUSA

Nijar ta yi allawadai da take yarjejeniyoyin da ke da nasaba da haka da fitar da man fetur din Nijar a cikin wata sanarwar CNSP

2024-06-10 15:43:50 CMG Hausa

A jamhuriyyar Nijar, kwamitin ceton kasa na CNSP ya fitar da wata sanarwa ta gidan rediyo da talabajin na kasa RTN a jiya kan ci gaba da tsare kwararrun Nijar hudu na WAPCO da mataimakiyar shugaban kamfanin a birnin Cotonou na kasar Benin tun ranar 5 ga watan Junin shekarar 2024. 

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ita dai wannan sanarwa ta fara da cewa, wadannan yarjejeniyoyi sun tsara sufurin man fetur tsakanin Nijar da Benin, babu inda suka kawo wani tsaiko ko wata hujjar hana tsarin sufuri a kai a kai. Babu wani dalili daga bangarorin da zai kawo wani cikas ga wannan sufuri. Ko yaki ya barke tsakanin Nijar da Benin, ba zai hana wannan sufuri ba.

Ke nan babu wata alaka da matakin Nijar na rufe iyakarta tare da kasar Benin bisa dalilin tsaro, matakin Nijar bai hana aikin tsarin sufurin man fetur tsakanin kasashen biyu, a cewar kakakin CNSP.

Kuma dukkan wadannan matakai an tanade su cikin kudurin doka mai lamba 22.4 game da yarjejeniyoyin da aka sanya hannu tsakanin kasashen biyu da WAPCO.

Kome zai faru, Nijar zata daukar dukkan matakan da suka wajaba domin ganin an sako ‘yan kasarta da aka yi garkuwa da su, da kare ‘yancinta da muhimman maradunta.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.