logo

HAUSA

Inma Gonzalez: “A yayin da nake a kasar Spaniya, sai na kuduri aniyar zama a kasar Sin”

2024-06-10 19:52:24 CMG Hausa

Madam Ima Gonzalez, ‘yar kasar Spaniya, shugabar dakin karatu na Cervantes dake birnin Shanghai dake gabashin kasar Sin, ta shafe sama da shekaru 40 tana zaune a kasar ta Sin, inda ta shaida manyan sauye-sauye da kasar ta samu sakamakon manufar da kasar ta sa a gaba ta yin kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, kana ta taka muhimmiyar rawa wajen yin cudanyar al’adu a tsakanin kasashen Spaniya da Sin. To, masu sauraro, a cikin shirinmu na yau, za mu kawo muku labari ne game da wannan baiwar Allah, mai suna Ima.

Madam Ima Gonzalez, shugabar dakin karatu na Cervantes dake birnin Shanghai, ta shafe sama da shekaru 40 tana zaune a kasar Sin, ta ce tun tana karama take sha'awar sanin kasar Sin mai ban mamaki. Lokacin da take kasar Spaniya, ko da yaushe tana da tunanin cewa, za ta iya rayuwa a kasar ta Sin. A wannan lokacin, ta yi iyakacin kokarinta don sanin komai game da Sin, kuma daga falsafar kasar zuwa wasan Kungfu na kasar, dukkansu sun burge ta kwarai da gaske.

Madam Ima ta ce, a lokacin da take karama, ta fara karanta wasu litattafai da suka shafi kasar Sin, wadanda suka gabatar da al'adun kasar Sin, fasahar kasar, da fadi-ka-mutu na kasar, da ma wadanda suka bayyana ilmin falsafa da adabin kasar, da dai sauransu. Daga lokacin, ta fara sha’awar kasar Sin sosai. Ta kara da cewa, ta kan kalli wasu wasannin kwaikwayo dangane da wasan Kungfu na kasar Sin a yayin da take Spaniya, don haka, ta fara koyon Kungfu a lokacin.

A shekarar 1979, Ima, a matsayinta na daya daga cikin rukuni na farko na daliban kasashen waje da suka samu karbuwa daga wajen kasar Sin, ta zo jami'ar koyon harsuna ta Beijing domin koyon Sinanci, daga nan ne kuma ta soma sabuwar rayuwarta a wannan kasa da take so.

Ima ta ce, a lokacin farko da ta zo kasar Sin don yin karatu, babu daliban kasashen waje da yawa a kasar. Don haka, a ko ina da kake tafiya, mutane suna sha’awarka sosai, suna son hira da kai, har ma wasu suna son daukar hoto tare da kai. A ganin Ima, wannan abu ne mai ban sha’awa gare ta.

Mijin Ima, dan kasar Sin ne kuma makadi ne a fannin wake-wake da kide-kide. Ta tuna da cewa, ita da mijinta sun taba taimakawa makada da yawa na kasar Sin wajen gudanar da kananan bikin kide-kide a wurin shan iska na Ritan da dakin cin abinci na Maxim da ke birnin Beijing a wancan lokacin.

Ima ba wai kawai ta taimakawa kungiyoyin kide-kide na kasar Sin wajen shirya bukukuwan kide-kide da wake- wake a nan kasar Sin ba, har ma ta gudanar da nune-nunen zane-zane na fasahar Sinawa a kasar Spaniya. A shekarar 1995, ta tsara tare da shirya baje kolin kayayyakin fasahar zamani na kasar Sin a Barcelona, wanda ya haifar da gagarumin martani a nahiyar Turai, kuma ya jagoranci Sinawa fasihai na zamani fiye da 30 zuwa dandalin duniya.

Ima ta bayyana cewa, wannan nune-nunen ba kawai ya jawo hankali sosai a cikin kasar Spaniya ba, har ma ya samu amincewa daga wajen nahiyar Turai baki daya. Domin a wancan lokacin, babu damammaki da yawa ga kasashen yamma ta fahimtar fasahar zamani ta kasar Sin, a sabili da haka, mutanen yammacin duniya kalilan suka san fasahar kasar Sin. Ko da yake fasahar yammacin duniya ta yi tasiri ga fasihan kasar Sin da ke halartar bikin baje kolin, amma abubuwan da suka nuna, na cike da halaye da abubuwa masu sigar kasar ta Sin, suna da halin musamman sosai ga masu kallo na Turai.

Ko shirya bukukuwan kide-kide da wake-wake ga kungiyoyin kide-kide na kasar Sin, ko kuma shirya bukukuwan baje koli ga masu fasahar kasar a Spaniya, duk ayyukan da Ima ta yi, abubuwa ne da take sha’awa sosai, a cewarta, tana farin ciki sada su da juna don yin mu’ammala.

Ima ta shafe shekaru sama da arba’in tana nazarin tarihi da al'adun kasashen Sin da Spaniya. Ta ce, mu'amalar da aka yi tsakanin kasashen Spaniya da Sin tana da dadadden tarihi, kuma a tarihi, 'yan kasar Spaniya da dama sun taba ba da gudummawa wajen sada zumunta a tsakanin kasashen biyu. Ima tana son mayar da su a matsayin abin koyi gare ta.

Daga kwamishiniya a fannin al'adu ta ofishin jakadancin Spaniya da ke kasar Sin, zuwa shugabar reshen kwalejin Cervantes a birnin Beijing, zuwa ma shugabar dakin karatu na Cervantes dake birnin Shanghai, a cikin shekaru fiye da arba'in da suka wuce, madam Ima ta himmatu wajen yin mu'amalar al'adu tsakanin kasashen Spaniya da Sin, inda ta shaida yadda ake zurfafa yin mu'amalar al'adu tsakanin kasashen biyu.

Ima ta bayyana cewa, babban nauyin dake bisa wuyanta a ko da yaushe shi ne kafa gadar yin mu’ammala a tsakanin Spaniya da Sin. Yanzu haka, mutane suna sha’awar koyon Sinanci a kasar Spaniya, har ma an riga an kafa kwalejojin Confucius kimanin 10 a kasar. Kaza lika, mawallafa ‘yan Spaniya da yawa sun fara wallafa litattafan da suka shafi adabin kasar Sin na lokacin da da na yanzu, wadanda aka fassara daga Sinanci zuwa harshen Spaniyanci. Don haka, Ima da abokan aikinta sun shirya jerin tarurruka game da fassara harshen Spaniya da koyar da Sinanci.

Madam Ima ta ga yadda aka yi kwaskwarima a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje a nan kasar Sin, kuma shaida yadda Sinawa ke farin ciki da shigar da kasar Sin kungiyar cinikayya ta duniya, kana ta yi fari ciki sosai tare da Sinawa da ganin Beijing ya cimma nasarar karbar bakuncin shirya wasannin Olympics na shekarar 2008. Lallai ta ga yadda wannan kasa ke samun ci gaba da wadata a sabon zamani. Ima ta ce, ta yi sa’a kwarai da gaske, saboda ta gan manyan sauye-sauye a wata kasa, wannan ya ba ta mamaki sosai.

A karshe dai, madam Ima ta ce, ko da yake akwai nisa a tsakanin kasashen Sin da Spaniya, amma kasashen biyu suna da halin musamman iri daya, don haka, suna da dangantaka mai kyau a tsakaninsu, tana fatan ci gaba da yin aiki wajen karfafa yin cudanya da mu’ammalar al'adu tsakanin kasashen biyu a nan gaba.