logo

HAUSA

Masana'antun samar da kayayyakin masarufi na gudana cikin wani yanayi mai armashi a kasar Sin

2024-06-10 15:10:21 CMG Hausa

Sabbin alkaluman da hadaddiyar kungiyar masana'antun sarrafa kayayyakin masarufi ta kasar Sin ta gabatar sun nuna cewa, cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, bangaren masana'antun samar da kayayyakin masarufi na kasar Sin ya gudana cikin wani yanayi mai armashi, inda kudin shigar da aka samu a wannan bangare ya kai kimanin kudin Sin RMB Yuan triliyan 7, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 966, jimillar da ta karu da kashi 2.6% bisa ta makamancin lokacin a bara.

An ce dalilin da ya sa ake dada samun karuwa a bangaren samar da kayayyakin masarufi a kasar Sin, shi ne wasu matakai da gwamnatin kasar ta dauka na neman ingiza bangaren sayayya, matakan da suka hada da ba da tallafi ga mutanen da suke neman maye gurbin tsoffin kayayyaki da wani sabo, da samar da karin nau'ikan kayayyakin masarufi, da tabbatar da ingancin kayayyaki, da yayata tamburansu, da dai sauransu, wadanda suka yi amfani wajen ingiza sayayya, musamman ma a bangaren sayen abinci, da kayayyakin latironi, da kayayyakin amfanin gida, da dai makamantansu. (Bello Wang)