logo

HAUSA

An gudanar da bikin janye sojojin Amurka daga janhuriyar Nijar

2024-06-09 15:01:12 CMG Hausa

A ranar Juma’a 7 ga watan nan ne aka gudanar da bikin ficewar sojojin Amurka daga janhuriyar Nijar, a sansanin sojojin dake birnin Yamai fadar mulkin kasar, bikin da ya samu halartar wasu manyan hafsoshin dake wakiltar rundunar sojojin Nijar, gami da sojojin Amurka dake da sansanoni daban daban a kasar ta Nijar.

A cewar bangaren rundunar sojojin Nijar, tun bayan da kasashen 2 suka daddale yarjejeniyar janyewar sojojin Amurka a watan Mayun da ya gabata, tuni sojojin Amurka 269 cikin jimillar 946 dake kasar suka riga suka bar janhuriyar Nijar, tare da kayayyaki da na’urorin su. Kana a wajen bikin da ya gudana a ranar Juma’a, dukkan bangarorin 2 sun jaddada bukatar cika alkawarin da aka dauka, na kammala aikin janye sojojin Amurka kafin ranar 15 ga watan Satumba mai zuwa. (Bello Wang)