Adadin iskar gas da aka yi amfani da ita a Sin a watanni 4 na farkon bana ya karu da kaso 11.9
2024-06-09 20:15:20 CMG Hausa
Yayin da kasar Sin ke kara kaimin bunkasa samar da ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, adadin iskar gas da aka yi amfani da ita a kasar cikin watanni 4 na farkon shekarar bana, ya karu da kaso kaso 11.9 bisa dari, idan an kwatanta da na makamancin lokaci na bara.
Alkaluman hukumar bunkasa ci gaba da aiwatar da sauye sauye ta kasar sun nuna cewa, adadin iskar gas din da aka yi amfani da ita tsakanin watan Janairu zuwa Afirilun bana, ta kai kyubik mita biliyan 143.73, wanda hakan ya nuna karuwar kaso 11.9 bisa dari a shekara. (Saminu Alhassan)