Kasar Sin ta kara kokarin kare kayayyakin tarihi
2024-06-09 15:23:12 CMG Hausa
Hukumar gabatar da kararraki mai matsayin koli ta kasar Sin, a jiya Asabar, ta fitar da wani rahoton bincike kan wasu lamurran karya doka guda 8, da suka shafi lalata kayayyakin tarihi, da neman mallake su ta haramtacciyar hanya da dai sauransu, ta hakan ya yi jagora ga ayyukan kananan hukumomin gabatar da kara dake wurare daban daban na kasar.
A cewar hukumar, ta riga ta nazarci ayyukan gabatar da kararraki bisa wasu lamurran keta doka fiye da 17000 da aka yi, wadanda suka shafi aikin kare kayayyakin tarihi, tun daga watan Oktoba na shekarar 2019.
Ban da haka, hukumar ta gabatar da kararraki mai matsayin koli, ta yi alkawarin ci gaba da karfafa tsare-tsaren shari'ar kasar ta fannin kare kayan tarihi, da neman dawo da kayayyakin tarihin kasar dake ketare zuwa gida.
A kasar Sin, a duk ranar Asabar ta biyu ga watan Yunin kowacce shekara, ake bikin ranar musamman da aka kebe don yayata tunanin kare al'adu, da kayayyakin tarihi na kasar. (Bello Wang)