logo

HAUSA

An kaddamar da sufurin jirgin kasa na dakon kaya kai tsaya daga Legos zuwa tashar tsandauri ta Dala Dry port dake Kano

2024-06-09 15:32:11 CMG Hausa

Jirgin kasa na dakon kaya daka Legos ya fara zuwa tashar tsandauri ta Dala Dryport dake jihar Kano bayan shekara guda da kaddamar da tashar.

Jirgin ya isa tashar ne ranar alhamis 6 ga wata dauke da kwantainoni 40 a matsayin gwaji na farko, inda ya taso daga tashar ruwa ta Apapa dake legos.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahato. 

A cikin watan janairun shekara ta 2023 ne gwamnatin da ta gabata ta kaddamar da sabuwar tashar bayan da kamfanin gine gine na kasar Sin CCECC ya samu nasarar kammala gyaran layin dokon jiragen dakon kayan daga Legos zuwa Kano.

A lokacin da yake kaddamar da fara zurga-zurgar jiragen , ministan sufuri na tarayyar Najeriya Sanata Sa`idu Ahmed Alkali ya ce babu shakka kaddamar da fara zurga zurgar jiragen daga Legos zuwa Kano a arewacin Najeriya zai taimaka matuka wajen rage yawan haduran motocin dakon kaya da kuma lalacewar manyan hanyoyin mota na kasar, haka zalika zai taimakawa kokarin da gwamnati ke yi wajen ragen cunkoson kayayyaki a tashar ruwa ta Apapa.

Ministan sufurin na tarayyar Najeriya ya yabawa kamfanin na kasar Sin saboda kokarin da ya nuna wajen kammala gyara layin dogon tare kuma da hada shi da tashar dakon kayan ta Dala Dryport dake unguwar Zawachiki a jihar Kano.

Sanata Ahmed Alkali ya ce baya ga wannan aikin da aka kammala na gyaran layin dogon dakon kaya daga Legos zuwa Kano.

“Ina kuma farin cikin sanar da ku cewa aikin shimfida layin dogo daga Lagos zuwa Kano da kuma Kano zuwa Maradi a janhuriyyar Nijar yana gudana kamar yadda ake bukata kuma cikin hanzari, haka kuma saboda gamsuwa da wannan aiki, kwanan nan ma gwamantin tarayya ta sake fitar da Karin kudi domin tabbatar da kammala aikin layin dogo daya taso daga Kaduna zuwa Kano.(Garba Abdullahi Bagwai)