logo

HAUSA

Kungiyar D-8 ta yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a Gaza

2024-06-09 15:34:24 CMG Hausa

Ministocin harkokin wajen kasashen kungiyar D-8, sun yi kira da a gaggauta dakatar da bude wuta a zirin Gaza ba tare da gindiya wani sharadi ba. Ministocin wajen kasashen kungiyar 8, sun yi kiran ne yayin taron da suka gudanar jiya Asabar a birnin Istanbul na kasar Türkiye.

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu na kasar Türkiye, ya rawaito cewa, ministocin ta wata sanarwar bayan taron da suka fitar, sun ce "Suna neman Isra’ila da ta dakatar da kaiwa Falasdinawa hare hare, nan da nan, ba tare da gindaya wani sharadi ba".

Sanarwar ta kuma kara da cewa, kasashe mambobin kungiyar ta D-8, za su samar da cikakken tallafi ga bukatun Falasdinu na zama mamba a MDD, da fafutukar samun cikakken ikon mulkin kai.

An kafa kungiyar hadin gwiwar samar da ci gaba ta kasashe 8 ko D-8 ne a shekarar 1997, kuma kungiyar ta kunshi kasashen Bangladesh, da Indonesia, da Iran, da Malaysia, da Masar, da Najeriya, da Pakistan da kuma Türkiye.  (Saminu Alhassan)