Sin na tallafawa matakan bunkasa tattalin arzikin teku da jagoranci a fannin
2024-06-09 16:05:42 CMG Hausa
Mataimakin ministan ma’aikatar albarkatun kasa, kuma shugaban sashen lura da harkokin teku na kasar Sin Sun Shuxian, ya ce Sin ta cimma sabon matakin bunkasa tattalin arzikin teku, tana kuma yayata hadin gwiwa, da kawance a harkokin da suka shafi jagorancin fannin tsakanin sassan kasa da kasa.
Sun Shuxian, wanda ya bayyana hakan a jiya Asabar, yayin bikin ranar teku ta duniya, wadda aka gudanar a birnin Xiamen, na lardin Fujian dake gabashin kasar Sin, ya ce alkaluman hukuma sun nuna cewa, darajar tattalin arzikin teku ta kasar Sin, ta kai kaso kusan 8 bisa dari cikin jimillar GDPn kasar, tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, wato a wa’adin aiwatar da shirin raya kasar Sin na shekaru biyar-biyar karo na 14.
Jami’in ya kara da cewa, a shekarar 2023, darajar tattalin arzikin teku na kasar Sin ya kai kudin kasar yuan tiriliyan 9.9, kimanin dalar Amurka tiriliyan 1.39, wanda hakan ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita bunkasar tattalin arzikin kasar.
Kaza lika, alkaluman ma’aikatar albarkatun kasa sun nuna cewa, a rubu’in farko na shekarar bana, mizanin yawan sundukan fitar da hajoji na cinikayyar waje ta kasar Sin, a tashoshin tekun kasar ya karu da kaso 11 bisa dari a shekara guda, sakamakon farfadowar bukatun waje, da raguwar da aka fuskanta a fannin, a shekarar da ta gabace ta.
Har ila yau, mataimakin ministan ya ce domin ingiza ci gaban kasashe masu makomar bai daya a fannin cin gajiyar albarkatun teku, kasar Sin ta sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa a wannan fanni, tare da kasashe sama da 50, da ma wasu hukumomin kasa da kasa. (Saminu Alhassan)