logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sha alwashin ceto masu hakar ma’adinan da rami ya fufta da su a jihar Niger

2024-06-08 16:38:58 CMG Hausa

Ministan ma’aikatar bunkasar harkokin ma’adinai a tarayyar Najeriya Mr. Dele Alake ya ce gwamnati ta kara tura kwararru kan sha’anin ceto zuwa yankin da aka samu hatsarin ruftawar ramin hakar ma’adinai a yankin Galkago da ke karamar hukumar Shiroro a jihar Niger.

Ministan ya tabbatar da hakan ne ranar Laraba 5 ga wata lokacin da ya kai ziyarar jaje ga gwamnati da al’ummar jihar Niger game da faruwar wannan hatsari, ya ce gwamnati za ta so a ce an ceto dukkannin ragowar mutanen da ransu, kasancewar yanzu haka wasu daga cikin su suna babban asibitin garin Mina.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Adadin masu hakar ma’adinai 30 ne hatsarin ya ritsa da su tun a ranar Litinin da ta gabata, inda ma’aikatan ceto ke ci gaba da aikin ganin sun fito da su.

Ministan ma’adinan na tarayyar Najeriya ya ce hakika gwamnati ta damu mutuka bisa samun labarin wannan hadari, inda ya jaddada kudurin cewa daga yanzu wajibi duk wani kamfanin hakar ma’adinai ya tanadi matakan kariya ga ma’aikatansa daga cin karo da duk wani hatsari da zai iya faruwa sakamakon sakacin dan adam.

Ya tabbatar da cewa nan gaba gwamanti ba za ta sake baiwa wani kamfanin hakar ma’adinai lasisi ba muddin ya gaza nuna ingantattun matakai na kare lafiyar ma’aikatan sa, kuma sai lallai an gudanar da bincike a kan yanayin filin hakar ma’adinan, ya ce hakar ma’adinai ta amfani da tsoffin kayan aiki da aka daina ya yi barazana ne babba.

“Babu yadda za mu yi da ruwan sama mai yawa wanda yana daga cikin abun da ya haifar da ruftarwar ramin, amma abun da muke da iko a kan sa shi ne kayayyakin aikin hakar ma’adinan na zamani masu inganci da ya kamata a tanada a ramukan hakar ma’adinan, wadanda za su iya rage munmunan tasirin duk wani hatsari da ka iya faruwa ga ma’aikata.” (Garba Abdullahi Bagwai)