logo

HAUSA

Hukumomin Nijar sun maida martani bayan tsare mataimakiyar darektan kamfanin WAPCO da abokan aikinta hudu a Benin

2024-06-07 09:55:48 CMG Hausa

A ranar jiya Alhamis 6 ga watan Yunin shekarar 2024 da yamma an gudanar da wani taron manema labarai a ma’aikatar shari’a da ke birnin Yamai, na hadin gwiwa tsakanin ministan man fetur Mahaman Moustapha Barke da kuma ministan shari’a Alio Daouda kan wasu ma’aikatan Nijar da aka tsare a Benin.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

Abin da ya fito karara a yayin wannan taron menama labarai shi ne cewa, Nijar ta baiwa hukumomin kasar Benin wa’adin ’yan sa’o’i domin da su saki manyan jami’an kasar na kamfanin WACPO suka kama, idan ba haka ba, kasar Nijar za ta rufe bututun manta.

Mataimakiyar darektan WACPO madam Moumouni Ibra Hadiza da wasu ma’aikanta hudu ’yan Nijar sun yi tafiya zuwa kasar Benin da sunan Nijar domin sanya ido kan lodin man fetur da za’a yi cikin jirgin ruwan dakon man fetur a tashar ruwan Seme ta kasar Benin. Sai dai kuma, ’yan sanda sun kama wadannan jami’ai a tsahar ruwan Cotonou a ranar Laraba 5 ga watan Junin shekarar 2024.

A yayin wannan taron ’yan jarida, ministan man fetur Mahaman Moustapha Barke ya bayyana cewa, jirgin ruwan dakon man fetur ba zai sake yin lodi ba, ba za mu sake tura man fetur ba cikin bututun man har sai Benin ta girmama alkawuran da ta dauka.

Hukumomin kasar Nijar sun tabbatar da mutanenta su biyar, ana ci gaba da tsare su a kasar Benin, bisa zirgin cewa sun ratsa kasar ta Benin ba tare da izni ba. (Mamane Ada)