Sin na fatan Amurka na yin wani abun a zo a gani na tallafawa ci gaba da farfadowar nahiyar Afirka
2024-06-07 20:19:21 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce abu ne mai sauki wani ya soki wasu, amma abu ne mai wahala ya iya kyautatawa sama da wadanda yake suka.
Mao Ning ta yi tsokacin ne a yau Juma’a, yayin taron manema labarai da ta jagoranta, lokacin da take mayar da martani ga kalaman suka da aka jiyo shugaban Amurka Joe Biden ya yi a baya-bayan nan, kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya. Jami’ar ta ce ana fatan Amurka za ta samar da kudade na hakika, domin bunkasa ci gaban nahiyar Afirka da kuma farfado da nahiyar.
Mao Ning, ta ce tun kaddamar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya shekaru sama da 10 da suka gabata, Sin ta sanya hannu kan takardun hadin gwiwa sama da 200 masu nasaba da shawarar, tare da kasashe sama da 150, da hukumomin kasa da kasa sama da 30, wanda hakan ya haifar da alfanu mai tarin yawa ga al’ummun kasashen, kana shawarar ta samu karbuwa sosai tsakanin al’ummun kasa da kasa.
Mao Ning ta kara da cewa, nahiyar Afirka daya ce daga wurare mafiya shiga a dama da su a gina shawarar. Albarkacin shawarar, kasashen Afirka da dama sun cimma nasarar gina manyan hanyoyin mota irinsu na farko, da gadojin teku irinsu na farko, da yankunan masana’antu irinsu na farko. Kana an gina cibiyar yaki da cututtuka irinta ta farko dake da cikakkun kayan aiki dake iya amfanar daukacin nahiyar. (Saminu Alhassan)