Sin na adawa da aniyar Amurka ta sayarwa yankin Taiwan makamai
2024-06-07 21:30:16 CMG Hausa
Kasar Sin ta bayyana adawarta ga aniyar Amurka, ta sayarwa yankin Taiwan makamai, tana mai kira ga bangaren Amurka da ya janye wannan aniya nan take.
Ma’aikatar tsaron kasar Sin ce ta bayyana hakan a Juma’ar nan, a matsayin martani ga amincewar da ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta yi, da batun sayarwa yankin Taiwan makamai na dala miliyan 300.
Da yake tsokaci kan lamarin, kakakin ma’aikatar tsaron Sin Zhang Xiaogang, ya ce Amurka ta keta alfarmar manufar kasar Sin daya tak a duniya, da yarjejeniyoyin hadin gwiwa 3 wadanda Sin da Amurka suka amince, musamman ma sanarwar ranar 17 ga watan Agusta, kuma hakan ya yi matukar keta hurumin ‘yancin kan kasar Sin, da tsaro da moriyarta. Kana hakan ya jefa tsaro, da daidaito a mashigin tekun Taiwan cikin halin rashin tabbas.
Zhang ya jaddada cewa, batun Taiwan jan-layi ne na farko da ba zai yiwu a tsallaka shi ba a dangantakar Sin da Amurka, Kuma ta hanyar ingiza aniyar ‘yan aware masu neman ’yancin kan Taiwan, sannu a hankali Amurka na hankada Taiwan cikin yanayi mai matukar hadari, wanda zai illata ita kanta Amurkan. (Saminu Alhassan)