logo

HAUSA

An yi tattaunawa tsakanin ministocin tsaron Sin da Amurka

2024-06-07 11:44:28 CMG Hausa

 Mamban majalisar gudanarwa ta kasar Sin kana ministan tsaron kasar Wang Xiaohong, ya tattauna da Alejandro Mayorkas, sakataren tsaron cikin gidan kasar Amurka ta kafar bidiyo a jiya Alhamis.

Wang Xiaohong ya bayyana cewa, kamata ya yi bangarorin biyu su tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashensu suka cimma, da nacewa ga ka’idar mutunta juna da daidaita mabambantan ra’ayoyi tsakaninsu, da cin moriya tare cikin hadin kai, da ma ci gaba da zurfafa hadin gwiwarsu a fannin yaki da miyagun kwayoyi da tesa keyar bakin haure, da dakile laifufuka da ake aikatawa tsakanin kasashe daban daban, da sauransu, ta yadda za a tabbatar da samun ci gaba na a zo a gani, wajen aiwatar da doka da shari’a. A cewarsa, dole ne Amurka ta mai da hankali kan muradun kasar Sin, da damuwarta, da ma daukar hakikanan matakai don bayyana matsayinta mai dacewa, da taka rawa wajen gaggauta karfafa hadin kan kasashen biyu.

Yayin tattaunawarsu, bangarorin biyu sun amince da kara tuntubar juna a fannin yaki da miyagun kwayoyi, da sauran ayyuka masu alaka da doka da shari’a. (Amina Xu)