logo

HAUSA

Xi Jinping ya gana da firaministan Pakistan da mataimakin shugaban kasar Brazil

2024-06-07 20:51:57 CMG Hausa

Da yammacin Juma’ar nan ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gana da firaministan kasar Pakistan Muhammad Shahbaz Sharif dake ziyara a kasar Sin.

A yayin ganawar tasu a nan birnin Beijing, shugaba Xi ya ce Sin da Pakistan abokai ne makwabta, wadanda suka yi imani da juna, suke kuma goyon bayan juna. Kaza lika, kasar Sin tana son ci gaba da nuna goyon baya ga kasar Pakistan, da fadada hadin gwiwarsu, da aiwatar da manufofinsu, da neman kyakkyawar makomarsu a sabon zamani, kuma ta hakan za a kara samar da gudummawar shimfida zaman lafiya, da zaman karko, da ci gaba da wadata a yankin.

Har ila yau a dai yau Juma’ar, shugaba Xi Jinping ya gana da mataimakin shugaban kasar Brazil Geraldo Alckmin wanda shi ma ke ziyara a kasar ta Sin. A yayin ganawarsu a nan birnin Beijing, shugaba Xi ya ce, Sin da Brazil manyan kasashe ne masu tasowa, kuma sabbin kasashe mafi samun ci gaba a duniya, don haka kasashen biyu suna da moriyar bai daya bisa manyan tsare-tsare, kana huldar dake tsakaninsu ta fi ta sauran sassa kyau, wadda ta zama abin misali a hadin gwiwar dake tsakanin kasashe masu tasowa, da kiyaye zaman lafiya a duniya baki daya.

Shugaba Xi ya ce ya kamata kasashen biyu su bi tsare-tsaren raya huldarsu, da kara samun moriyar juna a dukkan fannoni, da fadada hadin gwiwarsu, don sa kaimi ga daga matsayin sada zumuntarsu zuwa sabon mataki a sabon zamani.   (Zainab Zhang)