Sin na adawa da yunkurin Philippines na share wurin zaman dindindin a sashen tudun ruwa na Ren’aijiao
2024-06-07 20:44:05 CMG Hausa
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning, ta ce Sin na gargadin kasar Philippines, da kada ta yi yunkurin share wurin zama na dindindin a sashen tudun ruwa na Ren'aijiao, na yankin tekun kudancin Sin.
Mao Ning, ta yi jan kunnen ne a Juma’ar nan, yayin taron manema labarai da ta jagoranta, inda ta fayyace matsayin Sin game da sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, biyowa bayan zargin da dakarun tsaron teku na Philippines suka yi, cewa dakarun tsaron teku na Sin sun haifar da cikas, ga yunkurinsu na fitar da wani jami’in rundunar sojojin ruwan kasar maras lafiya, daga yankin tsibiran Nansha Qundao na Sin.
Jami’ar ta ce, idan da bangaren Philippines ya sanar da bangaren Sin kan lokaci, da dakarun na Sin sun baiwa na Philippines din damar shigar da muhimman abubuwan bukata na rayuwa, cikin jirgin ruwan yaki na Philippines din dake girke ba bisa ka’ida ba a sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, kuma da dakarun Philippines din sun samu iznin fitar da jami’in.
Mao ta kara da cewa, hakan ba ya nuni da cewa, bangaren Philippines zai yi amfani da wannan a matsayin dabarar shigar da kayayyakin gine-gine, cikin jirgin ruwan yakin dake girke a sashen tudun ruwa na Ren’aijiao, da nufin yin zaman dindindin a sashen tudun ruwa na Ren’aijiao. (Saminu Alhassan)