logo

HAUSA

Fadin gonakin da aka yi wa ban ruwa a kasar Sin ya zarce eka miliyan 26

2024-06-07 14:28:53 CMG Hausa

Mataimakiyar ministan kula da harkokin ruwa ta kasar Sin Zhu Chengqing ta bayyana a jiya Alhamis cewa, a bana, kasar Sin ta samar da ruwan da yawansa ya kai cubic mita biliyan 52.8 don gudanar da ayyukan gona, kuma fadin gonakin da aka yi wa ban ruwa a kasar ya zarce eka miliyan 26, matakin da ya samar da tushe mai inganci wajen tabbatar da girbi mai armashi a lokacin zafi.

A gun taron manema labarai da ma’aikatar kula da harkokin ruwa ta kasar Sin ta kira dangane da yadda ake tabbatar da samar da ruwa ga ayyukan gona, Zhu Chengqing ta ce, sakamakon gyare-gyaren da aka yi wa manyan sassan ban ruwa 598 a bara, an kara inganta tsarin ban ruwa, wanda ya taka rawa a ayyukan gona da aka gudanar a lokacin bazara na farkon bana. (Lubabatu Lei)