logo

HAUSA

Cinikayya tsakanin Sin da ketare ta karu da kaso 6.3

2024-06-07 14:30:18 CMG Hausa

Alkaluman da hukumar kwastam ta kasar Sin ta fitar a yau Juma’a sun nuna fadadar kayayyakin shige da fice na kasar Sin da kaso 6.3 ta fuskar takardar kudin yuan, a cikin watanni 5 na farkon bana.

A cewar hukumar, yawan kayayyakin da kasar ke fitarwa ketare ya karu da kaso 6.1 a kan na bara, daga watan Junairu zuwa Mayu, yayin da wadanda ke shigowa kasar ya karu da kaso 6.4. (Fa’iza Mustapha)