Wane irin tasiri magudin gwaje-gwaje da kamfanonin samar da motoci na Japan suka yi zai yi ga kasar?
2024-06-07 14:30:18 CMG Hausa
A kwanakin baya, an tono yadda wasu kamfanonin samar da motoci na kasar Japan biyar, ciki har da kamfanin Suzuki, suka tafka magudi a alkaluman gwaje-gwajen motoci da suka samar, lamarin da ya jawo hankalin sassa daban daban. Hayashi Yoshimasa, babban sakataren gwamnatin Japan ma ya amince da cewa, lamarin ba girgiza tushen tsarin tabbatar da ingancin motocin da ake samarwa a kasar kadai zai yi ba, har ma da amanar masana’antun hada motoci na kasar. Manazarta sun kuma yi nuni da cewa, kasancewar masana’antun samar da motoci babban ginshiki na masana’antun samar da kayayyaki na kasar, lamarin ka iya haifar da babban tasiri ga masana’antun cikin wani dogon lokaci.
Sakamakon faruwar lamarin, an bukaci kamfanoni da dama da su dakatar da samar da wasu samfuran motoci, abin da ya sa kamfanonin samar da motoci da ma kamfanonin samar da kayayyaki masu nasaba na kasar ke fuskantar miyagun hasarori. A halin yanzu, motocin da ake samarwa a Japan sun dauki kimanin kaso 2% na gaba dayan kayayyakin da ake samarwa a kasar ta Japan, don haka ma ana ganin cewa, wannan kalubalen da kamfanonin samar da motoci na Japan suke fuskanta zai iya haifar da mummunan tasiri ga karuwar GDP na kasar. (Lubabatu Lei)