logo

HAUSA

An kaddamar da katafaren kanti na farko da zai rinka aiki da wuta mai amfani da hasken rana tsawon awa 24 a Najeriya

2024-06-07 09:50:50 CMG Hausa

Hadin gwiwar wasu kamfanoni uku masu harkar fasahar samar da wuta ta amfani da hasken rana da suka hada da kamfanin Huawei na kasar Sin a ranar 5 ga wata sun samu nasarar kaddamar da katafaren kantina biyu na sayar da kayayyaki da za su rinka amfani da makamashin wutar solar  a Legos.

Rukunin kantinan na Just-rite super store sun kasance ne a unguwannin Ikorodu da Abule Agba, kuma za a fadada aikin sanya faranta zuko hasken rana da sauran na’urori a sauran rassa goma na kantin dake jihohin Oyo da Ogun nan da karshen watan gobe wanda zai samar da kaso 85 na adadin wutar da kantinan ke bukata.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.  

Wannan kanti dai shi ne irin sa na farko a yammacin Afrika wanda aka mayar da shi kan tsarin amfani da hasken rana, kuma adadin dala miliyan 6 da dubu dari 5 na jarin kamfanin Empower New Energy ya saka a aikin.

Kamfanin Huawei na kasar China shi ne ya gudanar da dawainiyar sanya farantan wutar da kuma batira kana da runbunan adana hasken rana a kantinan biyu da aka kaddamar karkashin jagorancin jakadan kasar Norway a Najeriya Mr. Svein Baera.

Mr. Ayodele Aderinwale shi ne shugaban rukunin kantinan na Justrite, “Saboda haka muddin kana son kasuwancinka ya ci gaba da gudanuwa ba tare da ya samu nakasu ba, kuma ka ririta kudi wajen tafiyar da harkokin kasuwanci wajibi ne ka sauya tsarin amfani da makamashin samar da wuta.”

A jawabinsa, babban shugaban kamfanin Huawei a Najeriya Mr. Chris Lu ya ce, sama da shekaru goma da suka wuce kamfanin na Huawei yake kasuwancin samar da na’uarar sarrafa wutar sola a kasashe daban daban na duniya.

“Daman dai mun fi mayar da hankali ne wajen samar da ingantattun kayayyakin solar da suka hada da na’urar Inbata da ta ESS da ta PCS kuma dukkannin kayayyakinmu suna da shedar karkon aiki na tsawon lokaci wanda wannan shi ne muhimmin abun da mai sayen kaya ke bukata.” (Garba Abdullahi Bagwai)