logo

HAUSA

Wang Yi ya gana da takwaransa na kasar Cuba

2024-06-07 11:22:57 CMG Hausa

 

Mamban ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, kana ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya gana da manzon musamman na shugaban kasar Cuba, kana ministan harkokin wajen kasar, Bruno Rodriguez a jiya Alhamis a nan birnin Beijing.

Yayin ganawarsu, Wang Yi ya ce, Sin na girmama matsayin da Cuba ke dauka na nacewa ga gaskiya da kin yarda da fin karfi da ake nuna mata, da kuma goyon bayan da take baiwa kasar Sin. Ya ce, Sin tana tsayawa tsayin daka wajen goyon bayan Cuba da ta kare tsarin mulkinta da kin amincewa da shisshige daga waje da adawa da shingayen da Amurka take sanya mata ba gaira ba dalili. Haka kuma, tana mai fatan kara hadin gwiwa da Cuba don tabbatar da matsaya daya da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da raya zumunci mai muhimmanci a tsakanin jam’iyyun siyasa na kasashen biyu, har ma da taka rawar gani wajen gaggauta sha’anin raya tsarin gurguzu a duniya da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

A nasa bangare, Bruno Rodriguez ya ce, yana godiya sosai ga goyon bayan da Sin take ba kasarsa na adawa da shingayen da Amurka ke kafa mata ba tare da wata hujja ba, da ma tallafin da Sin take baiwa kasar game da magance tafiyar hawainiyar tattalin arziki cikin gajeren lokaci. Bugu da kari, Cuba za ta nace ga dakon zumuncin dake tsakanin kasashen biyu da ka’idar “kasar Sin daya tak a duniya” ba tare da tangarda ba. (Amina Xu)