logo

HAUSA

Zimbabwe ta yaba da jarin da kasar Sin ta zuba a bangaren makamashi mai tsafta na kasar

2024-06-07 10:33:51 CMG Hausa

Hukumar kula da harkokin makamashi ta Zimbabwe (ZERA), ta yabawa adadin ayyukan makamshi mai tsafta, masu jarin kasar Sin, dake karuwa a kasar, tana mai cewa hakan ya taimaka wajen daidaitawa da rage matsi kan turakun lantarki na kasar.

Shugaban hukumar ZERA Edington Mazambani, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, hadin gwiwa tsakanin Sin da Zimbabwe a bangaren makamashi na karuwa, inda kamfanonin hakar ma’adinai na kasar Sin da dama ke kafa tashoshin makamashi mai tsafta domin tabbatar da samar da makamashi ga ayyukansu na hakar ma’adinai. (Fa’iza Mustapha)