logo

HAUSA

Shugabannin Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan sun taya juna murnar sanya hannu kan yarjejeniyar aikin layin dogo

2024-06-06 21:15:26 CMG Hausa

A yau Alhamis 6 ga watan nan na Yuni ne aka yi bikin sanya hannu kan yarjejeniyar aikin gina layin dogo tsakanin kasashen Sin da Kyrgyzstan da Uzbekistan.

Yayin bikin da ya gudana a birnin Beijing, shugaban kasar Sin Xi Jinping, da takwaransa na Kyrgyzstan Sadyr Zhaparov, da na Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev, sun taya juna murnar cimma yarjejeniyar ta kafar bidiyo.

A jawabinsa yayin bikin, Xi Jinping ya ce, layin dogon da zai hade kasashen uku, muhimmin aiki ne na dunkule sassan Sin da kasashen tsakiyar Asiya, kana aiki ne mai daraja ta fuskar hadin gwiwar kasashen 3, karkashin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Shugaba Xi, ya ce sanya hannu kan yarjejeniyar, tsakanin gwamnatocin kasashen 3, zai kafa ginshiki mai karfi na doka, domin cimma burin da aka sanya gaba, kuma za a tashi daga matsayin buri zuwa aiki na zahiri.

Kaza lika, aikin zai fayyacewa sassan kasa da kasa muhimmin kwazon kasashen 3 a fagen ingiza hadin gwiwa, da neman cimma nasarar bunkasa kai tare.

Layin dogon zai tashi daga birnin Kashgar na Xinjiang, zai shiga Uzbekistan ta Kyrgyzstan, kana a nan gaba akwai fatan tsawaita shi zuwa sassan yammaci da kudancin Asiya. Bayan kammalar aikin, layin dogon zai bunkasa hadewar kasashen 3 yadda ya kamata, tare da ingiza saurin bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al’ummun yankin.    (Saminu Alhassan)