logo

HAUSA

CPPCC ta lashi takobin raya tattalin arzikin kasuwa mai salon gurguzu

2024-06-06 15:30:52 CMG Hausa

Shugaban majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin (CPPCC) Wang Huning, ya ce majalisar za ta bayar da gudunmuwa ga raya ingantaccen tsarin tattalin arzikin kasuwa mai salon gurguzu.

Wang Huning wanda kuma mamba ne na zaunannen ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya bayyana haka ne lokacin da yake jawabin rufe taron karo na 7 na zaunannen kwamitin CPPCC karo na 14, a yau Alhamis.

Ya kara da cewa, tun bayan babban taron mambobin JKS na 18 a shekarar 2012, shugabancin jam’iyyar ke mayar da hankali kan daukakawa da inganta tsarin tattalin arzikin kasuwa mai salon gurguzu, wajen zurfafa gyare-gyare ta kowanne bangare ta hanyar daukar jerin matakai masu muhimmanci. (Fa’iza Mustapha)