Slovenia ta amince da Palasdinu a matsayin kasa a hukumance
2024-06-05 09:44:46 CMG Hausa
Majalisar dokokin Slovenia, ta kada kuri’ar amincewa da kudurin shaida Palasdinu a matsayin kasa, yunkurin da majalisar ke ganin zai taimaka wajen tsayar da rikicin Gaza.
Mambobi 52 daga cikin 90 ne suka kada kuri’ar amincewar, lamarin da ya sanya Slovenia wadda ba mambar dindindin na Kwamitin Sulhu na MDD ba, zama kasa ta 4 a Turai da ta amince da hakan a baya bayan nan, bayan kasashen Spaniya da Norway da Ireland. (Fa’iza Mustapha)