logo

HAUSA

An tattauna kan “gina ingantaccen tsarin tattalin arziki na kasuwanci mai salon gurguzu” a yayin taron zaunannen kwamitin CPPCC karo na 14

2024-06-05 11:40:57 CMG Hausa

An bude zama na 7 na zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta jama'ar kasar Sin (CPPCC) karo na 14 jiya Talata, a nan birnin Beijing, fadar mulkin kasar, inda aka yi shawarwari da tattaunawa kan harkokin siyasa da suka shafi “gina ingantaccen tsarin tattalin arziki na kasuwanci mai salon gurguzu”.

Wang Huning, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na Jam’iyyar Kwaminis ta Sin, kana shugaban majalisar CPPCC, shi ne ya jagoranci bikin bude taron. An kuma gayyaci Ding Xuexiang, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin koli na Jam’iyyar Kwaminis ta kasar, kana mataimakin firaministan gwamnatin kasar, da ya halarci taron tare da gabatar da rahoto.

A yayin bikin bude taron, an saurari rahotannin wasu kwamitocin musamman na CPPCC, game da gudanar da bincike kan yadda za a gaggauta yin gyare-gyare da inganta tsoffin masana'antu, da inganta gine-ginen kiyaye ruwa, da kara karfin aikin gona, da ciyar da sauyawar masana’antu masu kiyaye muhalli gaba, da hada kan yankin Guangdong da Hong Kong da kuma Macau, wajen shiga ayyukan raya shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da kuma aiwatar da dabarun kara inganta yankunan gwaji na cinikayya cikin ’yanci da dai sauransu. (Bilkisu Xin)