logo

HAUSA

Majalissar dattawan Najeriya ta ce za ta hanzatar zartar da kudurin dokar karin albashi da zarar an gabatar mata da shi

2024-06-05 09:11:53 CMG Hausa

Majalissar dattawan Najeriya ta tabbatar da cewa, ba za ta yi jinkiri ba wajen zartar da kudurin dokar karin albashi da zarar an gabatar mata da shi.

Shugaban majalissar Sanata Godswill Akpabio ne ya tabbatar da hakan yayin zaman majalissar na jiya Talata 4 ga wata, jim kadan da sanar da jingine yajin aikin da kungiyoyin kodagon kasar suka yi bayan zama da sakataren gwamnatin tarayya a daren Litinin 3 ga wata, sai dai ya ce akwai bukatar a samar da ginshiki mai kyau kafin fara aiwatar da sabon tsarin albashin domin amfanuwar daukacin ma’aikatan kasar a dukkan matakai.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Shugaban majalissar dattawan ta Najeriya ya ce, a lokutan baya zauren majalissar ya zartar da dokar mafi kankantar albashi na Naira dubu 30, to amma har yau kaso mafi rinjaye na jihohi da kananan hukumomi da sauran kamfanoni masu zaman kansu sun gaza biyan ma’aikatansu.

Ya ce, wajibi ne a yi la’akari da abun da ya faru a baya, domin maganin matsalolin da suke hana aiwatar da dokar tsarin albashi na bai daya a dukkan matakai, inda ya tabbatar da cewa, a shirye majalissar dokoki take ta ba da gudummawa wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka kulla tsakanin kungiyar kodagon da bangaren gwamnati.

Ko da yake majalissar dattawan ta Najeriya ta ankarar da ma’aikatar kasar cewa, muddin dai albashin ya yi sama sosai akwai yiwuwar da yawa daga ma’aikata su iya rasa aikin su.

Tun dai da safiyar ranar Talata 4 ga wata ne, kungiyar kodagon ta sanar da jingine yajin aikin nata zuwa kwanaki 5 domin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da suka kulla da gwamnati a yayin zaman shugabannin kungiyar da sakataren gwamnatin tarayyar Mr Geoge Akume.

Yarjejeniyar dai kamar yadda sakataren gwamnatin ya bayyana sun hada da, “Shugaban kasa ya amince cewa zai kara a kan ainihin tayin da yayi a baya na Naira dubu 60, sannan kwamitin da gwamnati ta samar a kan batun albashin zai rinka zama a kowacce rana har sai an kai ga samun daidaito, sannan kuma babu wani ma’aikaci da gwamnati za ta ci zarafinsa sakamakon shiga yajin aikin da ya yi.”

Yanzu dai al’amura sun fara koma yadda suke tun daga jiya Talata bayan sanar da jingine da yajin aikin da kungiyar kodagon kasar ta yi. (Garba Abdullahi Bagwai)