logo

HAUSA

Zargin da ke tattare da kalaman da ‘yan siyasar Philippines ke yi kan kasar Sin

2024-06-05 21:31:19 CMG Hausa

A baya-bayan nan ne shugaban kasar Philippines Ferdinand Romualdez Marcos ya gabatar da wani sako ga kasar Sin a gun taron tattaunawa na Shangri-La karo na 21, inda ya yi barazanar cewa, kasarsa ba za ta yi sassauci kan batun yanki ba. Dangane da haka, wakilin kasar Sin ya bayyana karara cewa, kasar Sin ta dade tana taka tsan-tsan a kan keta haddi da tsokan, amma akwai iyaka, tana fatan wasu kasashe za su fahimci muradunsu, su koma kan teburin tattaunawa da tuntubar juna.

Tun bayan kulla huldar diflomassiya tsakanin Sin da Philippines a shekarun 1970, gaba daya an kiyaye tasirin batun tekun kudancin kasar Sin kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Amma bayan da gwamnatin Marcos ta hau kan karagar mulki a shekarar 2022, jiragen ruwa na Philippines sun yi ta kutsawa cikin yankin teku na sashen tudun ruwa na Ren’aijiao da tsibirin Huangyan na kasar Sin, lamarin da ya haifar da koma-baya a dangantakar dake tsakanin Sin da Philippines.

Hasali ma, halin rashin hankali na gwamnatin Philippines yana da ma'ana. Bobby Tuazon, farfesa a jami'ar Philippines, ya bayyana cewa, Amurka ta dauki Marcos a matsayin wani makami ko ‘yar tsananta na yaki a fakaice. Domin kuwa saboda irin alkawurran tsaro na yaudara da Amurka ta yi, da yawan safarar tsoffin makamai, da kutsawa da tasirin Amurka a Philippines, ya sa gwamnatin Philippines ke son taka rawar gaggafa da kare game da martabar Amurka a harkokin yankin.

A yayin taron tattaunawar ta Shangri-La, an kuma lura cewa, ministan tsaron Amurka, Lloyd Austin, ya bai ce kome ba kan tambayar da Philippines ta yi masa game da matakan da Amurka za ta dauka idan wani abu mai nasaba da yarjejeniyar tsaron hadin gwiwa tsakanin Amurka da Philippines ya wakana, amma ya jaddada cewa, Amurkan za ta karfafa tattaunawa da kasar Sin don tabbatar da cewa irin wannan abu bai faru ba. Akasarin ra’ayin jama'a na ganin cewa, Amurka a fakaice ta bayyana cewa, bai cancanta ta yi fito-na-fito da kasar Sin ba. Ba zai yiwu ba ga Philippines da ta yi duk abin da take so sakamakon goyon bayan Amurka. (Yahaya)