logo

HAUSA

Za A Shirya Jarrabawar Neman Izinin Shiga Jami’a A Kasar Sin

2024-06-05 08:37:00 CMG Hausa

Tun bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, tsarin jarrabawar shiga jami'o'i ya samu sauye-sauye da dama, wanda ke nuni da sauye-sauyen falsafar ilmin kasa da bukatun raya al'umma. A shekarar 1952, kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin jarrabawar shiga jami'o'i ta kasa baki daya, Wanda ya zama silar kafa Gaokao a hukumance, wanda asalin manufarsa ita ce zabar kwararrun dalibai masu basira don shiga manyan makarantu domin ci gaba da karatu. Tun daga wannan lokacin, an ci gaba da yiwa tsarin jarrabawar neman izinin shiga jami’a ko Gaokao kwaskwarima  tare da kara inganta shi sau da yawa. To dai wannan tsarin jarrabawar neman izinin shiga jami’a anan kasar Sin ba wai kawai wani muhimmin ci gaba ne a fannin ilimi ba, sai dai ya kasance wani muhimmin abin da zai sauya makomar mutum a nan gaba. Wannan tsarin ilimi na kasar Sin mai matukar muhimmanci yana da alaka da makomar miliyoyin dalibai, kuma yana tasiri sosai kan hanyoyin gano basira da rarraba albarkatun ilimi a cikin al'umma, an kuma shirya tsaf domin gudanar da wannan jarrabawar neman izinin shiga jami’a anan kasar ta wannan shekarar da muke ciki.

Duba ga muhimmancin jarrabawar ta wannan shekara da kuma yawan daliban da zasu rubuta ne ya sanya mataimakin firaministan kasar Sin Ding Xuexiang, kuma mamban zaunannen kwamitin kula da harkokin siyasa na kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya duba aikin share fage na jarrabawar domin tabbatar da cewa komai yana tafiya bisa tsari. 

Rubuta wannan jarrabawar na bukatar wasu cancanta, alal misali cika shekarun da ake bukata na karatun sakandare, da shaidar shiga makaranta, da lafiyar jiki da dai sauransu. Ko da yake Sharudda na musamman na iya bambanta tsakanin larduna. Haka kuma ana bukatar dilibai su yi rajista ta yanar gizo a hunturun shekarar kafin jarrabawar, da dai sauran shirye-shirye masu muhimmanci.

Dalibai masu bukatu na musamman suma ba a barsu a baya ba, An musu tanade-tanade na musamman, wadanda suka hada da samar da takaddun jarrabawar Braille wato takardar musamman ga irin wadannan dalibai masu bukatu na musamman da kuma tallafi gare su kusan su 11,000 a cikin yankuna 11 na lardunan kasar. (Sanusi Chen, Mohammed Yahaya, Faeza Mustapha)