logo

HAUSA

Ana bukatar kiyaye muhalli a duniya amma ba bukatar ra’ayin ba da kariya ga cinikin kayayyakin kiyaye muhalli

2024-06-05 20:19:49 CMG Hausa

Yau ranar 5 ga watan Yuni, rana ce ta kiyaye muhallin duniya karo na 53. Game da batun kara sanya kudin harajin kwastam da wasu kasashe suka yi kan kayayyakin Sin masu taimakawa kiyaye muhalli, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, duniya daya kawai dan Adam yake da shi, ana bukatar kiyaye muhallin duniya tare. Ana bukatar kiyaye muhalli amma ba bukatar ra’ayin ba da kariya ga cinikin kayayyakin kiyaye muhalli.

Mao Ning ta bayyana cewa, kasar Sin ta kasance kasa mafi saurin kyautata ingancin iska a duniya, fadin bishiyoyi da kasar Sin ta shuka ya karu a shekaru 40 a jere, yawan iskar Carbon da Sin ta fitar bisa yawan GDP na kasar a shekarar 2023 ya ragu da kashi 35 cikin dari bisa na shekarar 2012, yawan na’urorin samar da wutar lantarki daga makamashi da aka iya sake yin amfani da shi a kasar Sin ya kai kashi 52.9 cikin dari bisa na dukkan na’urorin kasar. Ra’ayin ba da kariya ga cinikin kayayyakin kiyaye muhalli ba zai samar da makomar duniya mai kiyaye muhalli ba. Kasar Sin a shirye take ta yi kokari da hadin gwiwa tare da kasa da kasa wajen tabbatar da kiyaye muhalli a duniya. (Zainab Zhang)