Sojojin Isra’ila sun kaddamar da hare-hare ta sama da kasa a sansanin Bureji dake Gaza
2024-06-05 11:07:04 CMG Hausa
Kakakin rundunar sojin Isra’ila Avichay Adraee, ya ce bisa wasu bayanan sirri, jiragen yakin Isra’ila sun kai hare-hare wuraren da mayakan Hamas suke a sansanin ‘yan gudun hijira na Bureji dake tsakiyar Gaza, yayin da a lokaci guda kuma sojojin kasa, ke kai farmaki wurin.
A wani jawabi na daban, Avichay Adraee ya ce dakarun Isra’ila sun gudanar da wani samame a kewayen garin Sabra na Gaza a makon da ya gabata, inda suka gano makamai da rokoki ke harbawa, boye cikin wasu jakunkuna mallakar hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Palasdinu ta MDD (UNRWA). Sai dai, hukumar wadda ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da agajin jin kai a Gaza ba ta ce uffan ba game da ikirarin na Isra’ila.
A ranar 7 ga watan Mayu, sojojin Isra’ila suka fadada hare-hare a Rafah, inda suka ba Palasdinawa sama da miliyan 1 da rabi umarnin komawa garin Khan Younis da yankunan tsakiyar Gaza. Hukumar UNRWA ta yi kiyasin a yanzu haka, wadannan wurare na ba mutane kimanin miliyan 1.7 mafaka. (Fa’iza Mustapha)