COMESA da Bankin Duniya sun kaddamar da shirin samar da makamashi a Afrika
2024-06-05 10:41:12 CMG Hausa
Kungiyar bunkasa tattalin arzikin gabashi da kudancin Afrika da ake kira da Kasuwar Bai Daya ta Gabashi da Kudancin Afrika (COMESA), ta kaddamar da wani shiri dake da nufin gaggauta samar da makamashi ga fadin yankunan gabashi da kudancin Afrika.
Shirin na gaggauta samar da makamashi mai tsafta da dorewa, na da nufin samar da sabbin hanyoyin samun wutar lantarki ga mutane miliyan 100 cikin shekaru 7 masu zuwa. Shirin zai mayar da hankali ne wajen fadada hanyoyin samar da lantarki dake hade da turakun lantarki da wadanda ba sa hade da turakun, da na makamashi mai tsafta da fasahohin girki masu tsafta da kuma sauran nau’o’in makamashi.
Yayin kaddamar da shirin a birnin Lusaka na kasar Zambia, sakatare janar ta COMESA Chileshe Mpundu Kapwepwe, ta ce kasashen Afrika na bukatar jari mai yawa domin magance kalubalen makamashi da suke fuskanta. A cewarta, bisa hasashen Bankin Raya Afrika, ana bukatar kimanin dala biliyan 35 domin samar da makamashi na bai daya a Afrika, kawo shekarar 2030.
A nata bangare, Boutheina Guermazi, daraktar ofishin Bankin Duniya a kudu da hamadar Sahara, da Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afrika, ta bayyana shirin a matsayin muhimmi, wanda zai kawo gagarumin sauyi wajen taimakawa kasashen Afrika samar da wutar lantarki ga jama’arsu. Tana mai cewa, tabbatar da samar da makamashi mai karko da araha ga kowa, wani muhimmin bangare ne na manufofin bankin a nahiyar Afrika. (Fa’iza Mustapha)