logo

HAUSA

Shugaban kasar Nijar Abdourahamane Tiani ya gana da mukadashin ministan tsaron kasar Rasha

2024-06-04 15:14:10 CMG Hausa

Shugaban kasa, kana shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, birgadiye janar Abdourahamane Tiani ya tattauna a ranar Lahadi 2 ga watan Junin shekarar 2024 a fadar shugaban kasa da ke birnin Yamai da wata muhimmiyar tawagar sojojin kasar Rasha a karkashin jagorancin mukadashin ministan tsaron kasar Rasha kanal-janar Ynus Bek Yevkurov.

Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto. 

A rike cewa mukadashin ministan tsaron kasar Rasha ya samu ganawa da shugaban kasar Nijar a ranar 4 ga watan Disamban shekarar 2023. Wannan tawaga ta zo birnin Yamai, a cikin tsarin ziyarar aiki inda kuma ta samu tattaunawa tare da ministan tsaron kasar Nijar, janar din sojoji Salifou Mody.

A karshen wannan ganawa an sanya hannu kan wani kundin fahimtar juna tsakanin kasar Rasha da kasar Nijar, lamarin dake nuna da tabbatar da kyaukyauwar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Cikin tsarin karfafa wannan huldar dangantaka tsakanin wadannan kasashe biyu, a ranar 26 ga watan Maris din shekarar 2024, shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP ya yi wata tattaunawa ta tsawon sa’o’i ta wayar tarho tare da shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin. Tattaunawar da a yayinta shugabannin biyu suka maida hankali kan muhimman batutuwan da ke daukar hankalinsu da kuma batutuwan kasa da kasa.

Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.