logo

HAUSA

AU ta yi gargadi game da karuwar rikice-rikice da sauye-sauyen gwamnati ba bisa ka’ida ba a nahiyar

2024-06-04 09:36:45 CMG Hausa

Tarayyar Afrika (AU) ta yi gargadi game da munanan tasirin karuwar rikice-rikice da sauye-sauyen gwamnati da suka sabawa kundin tsarin mulki, wadanda ke barazana ga tushen demokradiyya da tsaron kasashen Afrika.

Wannan na kunshe ne cikin jawabin da Alhaji Sarjoh Bah, daraktan ofishin kula da warware rikice-rikice na sashen harkokin siyasa da zaman lafiya da tsaro na hukumar AU, ya gabatar yayin taro kan zaman lafiya da tsaro da ya gudana a hedkwatar kungiyar dake Addis Ababa na Habasha.

Alhaji Sarjoh Bah ya kara da cewa, nahiyar Afrika ta yi rashin sa’a na shaida karuwar rikice-rikice a yankuna kamar na kahon Afrika da Sahel da gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo.

Ya kuma jaddada cewa, irin wadannan al’amura, na samar da kafofin da kungiyoyin ta’adda da masu tsatsauran ra’ayi da wasu daga waje ke amfani da su wajen kara haifar da rikici a nahiyar, domin yin tsaiko ga ci gaban da ake samu ta fuskar zaman lafiya mai dorewa. (Fa’iza Mustapha)