logo

HAUSA

Kamfanonin kula da jigila da na layin dogo na Habasha za su hada hannu wajen zamanantar da bangaren jigila na kasar

2024-06-04 13:59:51 CMG Hausa

Kamfanin kula da layin dogon da ya hada Habasha da Djibouti (EDR) da kamfanin kula da harkokin jigilar kayayyaki (ESL), mallakin gwamnatin kasar Habasha sun rattaba hannu a jiya Litinin, kan yarjejeniyar hada hannu wajen zamanantar da bangaren jigilar kayayyaki na kasar.

Wani rahoto na kamfanin dillancin labarai na kasar Habasha, ya ruwaito Abdi Zenebe, babban jami’in kamfanin EDR na cewa, sabuwar hadin gwiwar za ta taimaka wajen inganta bangaren jigila na kasar ta gabashin Afrika ta hanyar amfani da ingantaccen tsarin hadin gwiwa.

A cewar rahoton, ana sa ran yarjejeniyar za ta kara yawan gudunmuwar da layin dogon wanda ke tsakanin Habasha da Djibouti ke bayarwa ga daukacin harkokin shige da fice na kasar.

A nasa bangare, Beriso Amelo, babban jami’in kamfanin ESL cewa ya yi, yarjejeniyar za ta ba kamfanonin EDR da ESL damar kara bayar da gudunmuwa mai ma’ana ga karin bangarorin tattalin arzikin Habasha.

A cewarsa, ta hanyar magance dukkan abubuwan dake tarnaki ga tsarin jigila na kasar, yarjejeniyar za ta saukaka wajen samar da ingantattun hidimomin sufuri.

Layin dogo mai tsayin kilomita 752 da ya hada Habasha da Djibouti, wanda Sin ta gina ya zama hanyar da aka fi so na jigilar kayayyakin da ake shige da ficensu. A cewar EDR, a yanzu haka, ana jigilar sama da kaso 15 cikin dari na daukacin kayayyakin da ake shige da ficensu a Habasha, ta wannan layin dogo. (Fa’iza Mustapha)