logo

HAUSA

Xi Jinping ya mika sakon murna ga sabuwar shugabar Mexico

2024-06-04 20:23:59 CMG Hausa

A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika sakon taya murna ga Claudia Sheinbaum Pardo da zama sabuwar shugabar kasar Mexico.

A cikin sakon, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, kasar Mexico muhimmiyar kasa ce a yankin Latin Amurka, kana ita ce sabuwar kasuwa a duniya, Sin da Mexico abokai ne bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni. A halin yanzu, ana raya huldar dake tsakanin kasashen biyu, da samun moriyar juna bisa manyan tsare-tsare da fifikonsu, kana sun shiga muhummin lokacin raya huldarsu. Sin ta dora muhimmanci sosai kan raya huldar dake tsakaninta da Mexico. Xi ya ce, a shirye yake ya ci gaba da yin mu’amala tare da shugaba Sheinbaum don raya huldar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi, ta hakan za a amfanawa jama’ar kasashen biyu baki daya. (Zainab Zhang)