logo

HAUSA

Masana fiye da 20 na MDD sun yi kira ga dukkannin kasashen duniya da su amince da kasancewar kasar Falasdinu

2024-06-04 14:36:38 CMG Hausa

Masana fiye da 20 na MDD sun fitar da sanarwa tare jiya Litinin a Geneva na Switzerland, inda suka yi kira ga dukkannin kasashen duniya da su amince da kasancewar kasar Falasdinu.

A cikin sanarwar, masanan sun bayyana cewa, kasashe mambobin MDD fiye da 140 sun riga sun amince da kasancewar kasar Falasdinu, suna cewa ya kamata dukkannin sauran kasashen duniya su ma su yi hakan.

Masanan suna ganin cewa, dole ne Falasdinu ta samu cikakken ikon kafa kasa mai cin gashin kanta, wanda ya hada da ikon rayuwa da tantance makomarta da ci gabanta cikin 'yanci a matsayin wata al’umma mai tsaro.

Masanan sun kara da cewa, amincewa da kasancewar kasar Falasdinu, muhimmin sharadi ne na cimma zaman lafiya mai dorewa a Falasdinu da yankin Gabas ta Tsakiya. Sun kuma yi kira da a dakatar da bude wuta a zirin Gaza nan take, da dakatar da kai hare-haren soja a birnin Rafah, dake kudancin zirin Gaza.

A cikin ’yan shekarun nan, an dakile kafuwar kasar Falasdinu, amma bangarori daban daban sun riga sun amince da kasancewarta a mtasayin wata kasa. A ranar 28 ga watan Maris na shekarar bana, gwamnatocin kasashen Norway da Spain da Ireland suka amince da kasancewar kasar Falasdinu daya bayan daya. Kafin wannan, Barbados, Jamaica, Trinidad da Tobago, Bahamas da sauran kasashen duniya, duk sun amince da kasancewar Falasdinu a matsayin kasa. (Safiyah Ma)