logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya za ta gudanar da taron gaggawa da shugabannin kungiyar kodagon kasar

2024-06-04 09:25:12 CMG Hausa

A kokarin dakile ci gaba da yajin aikin kungiyoyin kodagon kasar, gwamnatin tarayyyar Najeriya za ta gudanar da taron gaggawa da shugabannin kungiyoyin Kodago yau Talata 4 ga wata.

Hukumar lura da tsarin albashin ta kasar ce ta aike da takardun gayyatar taron ga shugabannin kungiyar da yammacin jiya Litinin, kuma za a gudanar da taron ne a harabar hukumar dake birnin Abuja.

Daga tarayyar Najeriya wakilinmu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto a game da halin da al’umar kasar suka shiga a sanadiyar yajin aikin da aka fara jiya. 

Idan dai za a iya tunawa an gaza samun daidaito tsakanin bangarorin biyu yayin taron da suka gudanar a ranar 31 ga watan jiya, inda gwamnatin tarayya ta kafe kan albashin naira dubu 60 yayin da ita kuma kungiyar Kodago ta tsaya lallai sai naira dubu 494.

Wannan kiki-kaka ya sanya ma’aikatan kasar shiga yajin aiki tun daga jiya Litinin, wanda yau Talata aka shiga rana ta biyu da wannan yajin aiki.

Yajin aikin na gama gari ya tsayar da al’amura a kasar, inda tun a jiyan ma’aikatan hukumomin samar da wuta suka katse layikan samar da wuta a duk kasar, sannan kuma bankuna da tasoshin jiragen sama da sauran ma’aikatu sun kasance a kulle.

Wannan hali ya sanya al’ummar kasar cikin halin kunchi, inda suke kira ga kungiyoyin kodagon da su sauya tunani tare da komawa zaman sulhu da gwamnati.

“Mutane suna shan wahala, babu ruwa babu wuta sannan kuma babu kudi.”

“Ba zan taba cewa gwamnatinmu gurbatacciya ce, gwamnatinmu tana da kyau, sai dai abun da ya kamace mu shi ne mu kasance masu hakuri.”

“Shawara ta ga gwamnati da kungiyar kodago shi ne yajin aikin ba shi ne mafita ba.”

Wasu al’ummomi ke nan a jihar Gombe suke kokawa a game da halin da wannan yajin aiki ya saka su. Haka kuma al’amarin yake a dukkan jihohin kasar. (Garba Abdullahi Bagwai)