logo

HAUSA

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya ya kira wata ganawar sirri da shugabannin kungiyar Kodagon kasar

2024-06-04 09:30:20 CMG Hausa

Sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya Geoge Akume ya kira ganawar sirri da shugabannin kungiyar kodagon kasar a daren jiya Litinin 3 ga wata a ofishinsa dake Abuja.

Daga Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto. 

Ita dai wannan ganawar gaggawa da sakataren gwamnatin tarayyar ya kira shugabannin kungiyar tana daya daga cikin jerin matakai da gwammatin kasar ke dauka domin kawo karshen yajin aikin ma’aikata a kasar wanda ya fara gurgutar da harkokin walwala da na tattalin arzikin Najeriya.

A wata sanarwar da hukumar lura da harkokin albashin ta kasar ta fitar jiya, ta nuna cewa za ta gana da shugabannin kungiyar a yau Litinin.

Ko da yake an hana manema labarai ziyartar wajen da ake gudanar da wannan taro da sakataren gwamnatin ya kirawo tare da sauran manyan jami’an gwamnatin kasar.

Amma kuma shugaban kungiyar Kodagon ta tarayyar Najeriya Mr Joe  Ajaero ya sanar a shafinsa na X cewar an gewaye harabar wurin taron nasu da sojoji, amma runduanr sojin kasar ta musanta hakan, inda ta bayyana cewa sojojin da suka kasance a wurin taron masu lura da lafiyar mashawarcin shugaban kasa ne kan al’amuran tsaron, Nuhu Ribado wanda shi ma yana daga cikin manyan jami’an gwamnatin da suka halarci taron na daren jiya Litinin. (Garba Abdullahi Bagwai)