Sin ta ki amincewa da Amurka ta sanar da kayyade biza kan jami’an gwamnatin yankin Hong Kong na kasar Sin
2024-06-03 20:47:34 CMG Hausa
A kwanakin baya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Amurka ya ba da wata sanarwa kan hukuncin da kotun yankin Hong Kong na kasar Sin ta yanke wa wasu mutane da suka aikata laifin yin yunkurin sauyin mulkin kasa, inda aka sanar da sabbin matakai don kayyade biza kan jami’an gwamnatin tsakiya ta kasar Sin da gwamnatin yankin Hong Kong na kasar Sin.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta yi nuni da cewa, Amurka ta yi watsi da ka’idar “kasa daya amma da tsari biyu”, da dokar kiyaye tsaron kasa na yankin Hong Kong, da yanayin demokuradiyya na yankin Hong Kong, da tsoma baki kan aiwatar da doka a yankin, da kuma daukar matakan kayyade biza. Abubuwan da Amurka ta yi sun tsoma baki kan harkokin cikin gida na kasar Sin, da sabawa ka’idojin dokokin duniya da ka’idojin huldar dake tsakanin kasa da kasa, kasar Sin ta ki amincewa da wannan.
Game da abubuwa masu kawo illa ga kasar Sin a cikin hadaddiyar sanarwa da aka bayar bayan taron ministocin tsaro na kasashen Amurka da Japan da Koriya ta Kudu da taron mataimakan ministocin harkokin wajen kasashen uku, Mao Ning ta bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau cewa, tarukan biyu sun yi yunkurin aiwatar da manufofinsu kan yankin tekun Indiya da tekun Pasifik, da tsoma baki kan batun yankin Taiwan da harkokin cikin gida na kasar Sin, da sake zargin kasar Sin kan batun yankin teku, da tada rikici a tsakanin Sin da kasashe masu makwabtaka, ayyukan sun sabawa ka’idojin huldar dake tsakanin kasa da kasa, kuma kasar Sin ta ki amincewa da wannan. (Zainab Zhang)