Shugaban kasa Abdourahamane Tiani ya saurari masu fama da nakasa game da makomar Nijar
2024-06-03 10:27:19 CMG Hausa
Shugaban kasar Nijar kuma shugaban kwamitin ceton kasa na CNSP, Abdourahamane Tiani ya gana a ranar Asabar 1 zuwa Lahadi 2 ga watan Junin shekarar 2024, tare da tawagar kungiyar mutane masu fama da nakasa ta kasa FNPH, a karkashin jagorancin shugabanta Idrissa Alzouma Maiga.
Daga birnin Yamai, abokin aikinmu Mamane Ada ya turo mana da wannan rahoto.
Wannan ganawa tana cikin tsarin tattaunawa da shugaban kasa ya fara tare da masu ruwa da tsaki da masu fadi a ji, da ma wakilan jama’a bisa manufar sauraren muhimman bukatan rukunonin al’ummar kasar Nijar baki daya.
Shugaban kungiyar nakasassu ta kasa ya shaidawa manema labarai jim kadan bayan wannan ganawar tasu, cewa shugaba Abdourahamne Tiani ya bayyana bukatar ganawa tare da su, domin sanin halin da suke ciki, da kuma sanin muhimman matsalolin masu fama da nakasa.
Shugaban kasa ya yi imani cewa, gina kasa dole sai da halartar dukkan rukunonin jama’a, ba tare da nuna bambanci ba domin halartar ’yan Nijar maza da mata ta zama wajibi.
Haka kuma wannan tattaunawa tare da shugaban kwamitin ceton kasa ta shafi kalubalen da kasar Nijar take fuskanta. Kuma muna fatan wannan ganawa da shugaban kasa ya kaddamar tare da masu ruwa da tsaki na al’ummomi za ta taimakawa wajen gina kasarmu, in ji shugaban kungiyar FNPH.
Haka zalika, Idrissa Alzouma Maiga ya bayyana cewa kowa ya san Nijar na fuskantar kalubale daban daban tare da nuna cewa shugaban CNSP ya bayyana fatansa na ganin cewa an hada da nakasassu wajen neman shawarwari.
Ba ma fatan a mai da mu dabara wajen aikin gina kasa, ya jaddada wa shugaban CNSP tare da nuna cewa nakasassu ba za su yi kasa a gwiwa ba, wajen cika nauyin da aka dora musu, in ji shugaban kungiyar masu fama da nakasa ta kasa.
Mamane Ada, sashen hausa na CMG daga Yamai a jamhuriyyar Nijar.