logo

HAUSA

Iyalin Yuan Zhaohui da Anita Jumekenova: Mutunta juna, fahimtar mabudin farin cikin iyali

2024-06-03 15:54:49 CMG Hausa


Yayin da yake jin dadin bunkasuwar kasuwanci a karkashin shirin shawarar ziri daya da hanya daya ta BRI, Yuan Zhaohui, daga Xi'an, babban birnin lardin Shaanxi dake arewa maso yammacin kasar Sin, ba wai kawai ya yi soyayya da Anita Jumekenova, 'yar kasar Kazakhstan ba, har ma ya yi aiki tare da ita, domin kafa kasuwanci ta yanar gizo  tsakanin Sin da Kazakhstan.

Silk Road City, sunan wani kamfanin kasa da kasa ne, dake gudanar da kasuwanci ta intanet, wanda ma'auratan suka kafa a shekarar 2015. Kamfanin ya kasance tamkar wata gada dake taimakawa wajen bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen biyu da zurfafa zumuncinsu. A shekarar 2020, ma'auratan sun samu lambar yabo ta abokantaka ta hanyar siliki.

Yuan Zhaohui ya bayyana cewa, “auren da na yi daga ketare ya samu alfanu da ci gaban kasar Sin, aiwatar da shirin na BRI ya ba da ma'ana mai kyau ga aure na, da ma sana'ata. Idan aure na nufin haduwar iyalai biyu, to ina ganin ma’aurata daga kasashe biyu na nufin haduwar kasashe biyu."

Yuan ya kara da cewa, "Akwai kamanceceniya ta al'adu da dama a tsakanin Sin da Kazakhstan, amma kuma akwai wasu bambance-bambance. A ko da yaushe muna mutunta juna da fahimtar juna, da kuma al'adun kasashenmu. Muna ganin hakan shi ne mabudin kiyaye farin ciki da zaman lafiya na iyali." Yuan ya ci gaba da cewa, "Na ga bambance-bambancen al'adu ba ya shafar hanyoyin sadarwarmu kwata-kwata. Hasali ma, al'adunmu da suka sha banban da juna suna taimaka mana sosai a auratayya da kuma sana'o'inmu."

A wurin aiki, Jumekenova ce ke kula da aikin sadarwa na yau da kullum da kuma gudanar da ayyukan da suka shafi tawagar ‘yan kasar Kazakhstan, Saboda ta saba da yanayin gida da kuma al'adu na Kazakhstan, da kuma sauran tsakiyar kasashen Asiya.

Yayin habaka dandalin kasuwancin ta kafar intanet na SRC SHOP na kamfanin, Jumekenova ta yi cikakken bayani ga tawagar aikin, kan al'adu da halayen mutanen tsakiyar Asiya. Don haka, a farkon matakai na bunkasa shafin, an yi la'akari da aiki da harshen mutanen gida, kuma an kirkiri tsarin shafin da tsarin aiki daidai da kyawawan ra'ayoyi da halaye na mazauna yankin. Dandalin kasuwancin ya samu karbuwa sosai a tsakanin mazauna yankin. 

A yayin da take tattaunawa kan aikin tarbiyar da yara, Jumekenova ta ce, Sinawa da ‘yan Kazakhstan duka suna mai da hankali sosai kan ilimin yara, kuma sun dage wajen samar da yanayi mai kyau na iyali ga yara, da raya kyawawan dabi'un yara na mutunta iyayensu da manyansu, da kula da kannensu, da kuma kasancewa a shirye don taimakawa wasu.

Jumekenova ta kara da cewa, “Na shafe fiye da shekaru 10 a kasar Sin, ina jin Sinanci sosai, kuma ina darajta al'adun kasar Sin sosai. Na hada al'adu da harsunan kasashen biyu, na samar da yanayin koyo na musamman ga danmu, Ina masa jagora ya koyi da'a, al'adu da dabi'u daban-daban na kasar Sin da Kazakhstan, kuma ina taimaka masa wajen sanin fasahohin mu’amala na mabambantan al'adu.” Kowace shekara, ma’auratan suna kai dansu zuwa Kazakhstan na ’yan watanni don ya koyi al’adu da yaren Kazakhstan.

Yuan da iyalinsa su kan yi bikin bazara wato bikin sabuwar shekarar gargajiyar Sinawa a kasar Sin. A lokacin bikin bazara, suna manna takardun fatan alheri, da hada abincin Jiaozi, da cin abincin dare tare da iyali a jajibirin sabuwar shekara, da kuma ziyartar shahararrun wuraren yawon bude ido a birnin Xi'an don kallon nune-nunen fitilun gargajiya.   

Haka kuma suna murnar sabuwar shekara kowace shekara a Karaganda, garin Jumekenova a Kazakhstan. Yuan ya ce, "’yan Kazakhstan sun yi imanin cewa, bukukuwa za su kawo musu arziki da kuma sa'a a duk shekara, kuma dukkan cuttuttuka, da rashin sa’a, da bala'o'i za su guje musu."

Tafiya tsakanin Xi'an da Kazakhstan ya fi dacewa tun ranar 21 ga watan Afrilu na shekarar 2023, lokacin da jirgin saman farko ya tashi daga Xi'an zuwa Astana, babban birnin Kazakhstan, wanda ya zama hanya ta hudu ta jigilar fasinjoji kai tsaye tsakanin Xi'an da tsakiyar Asiya da aka kafa a shekarar 2023, bayan kafa hanyoyin zuwa Almaty dake Kazakhstan, Bishkek na kasar Kyrgyzstan, da Tashkent na kasar Uzbekistan.

Yuan ya bayyana cewa, "Ni da matata mun yi farin ciki da jin dadin tashin jirgin kai tsaye tsakanin Xi'an da Astana. A baya, sai dai mu fara tashi daga Xi'an zuwa birnin Chengdu, daga bisani mu tashi zuwa Kazakhstan. Farawar zirga-zirgar jiragen sama kai tsaye ya kawo mana sauki sosai wajen tafiye-tafiye, kuma ya taimaka mana wajen bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen biyu."

Kamfanin Silk Road City yanzu yana da ma'aikata 51, a gida da waje, kuma akwai reshen kamfanin a Karaganda. Kamfanin ya fi tsunduma cikin kasuwancin ta kafar intanet wajen fice da shigen kayayyakin amfanin gona.

Jumekenova ta ce, "Mun yi sa'a da aka samar da manufofi masu dacewa da yawa, godiya ga shirin BRI. Tare da ingantattun tsarin samar da kayayyaki da sufuri, ta hanyar zirga-zirgar jiragen ruwa na Chang'an na Sin da Turai, muna da karin kwarin gwiwa wajen tinkarar habakar oda.”

Yuan kuma ya nuna cewa, “A nan gaba, za mu ci gaba da inganta wuraren ajiyar kayayyakinmu na ketare, da kafa cibiyar cinikayyar kayayyakin amfanin gona da sauran hajoji a Kostanay na kasar Kazakhstan, da fadada harkokin kasuwancinmu a karin kasashe da ke kan hanyar siliki."

Masu sauraro, da haka muka kawo karshen shirinmu na yau na In Ba Ku Ba Gida, da fatan kun ji dadinsa. A madadin Mohammad Baba Yahaya da ya fassara bayanin, ni Kande da na shirya muku shirin nake cewa a kasance lafiya daga birnin Beijing.(Kande Gao)