logo

HAUSA

Sin: Kalaman bangaren Philippines sun yi watsi da tarihi da gaskiya

2024-06-03 13:55:46 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin ya amsa tambayoyin ‘yan jarida, game da kalaman da shugaban Philippines Ferdinand Romualdez Marcos ya yi, a jawabin sa mai nasaba da batun tekun kudancin Sin a taron tattaunawa na Shangri-La.

Kakakin ya ce kalaman da suka fito daga bangaren Philippines ba su da tushe a tarihi, kana ba sa kan gaskiya. Ya ce kasar Sin tana da cikakken ikon mallakar tsibiran dake tekun kudancin Sin. Kasar Philippines ta gabatar da kara a kotun kasa da kasa ba tare da amincewar gwamnatin kasar Sin ba, don haka hukuncin da aka yi a kan batun shari'ar tekun kudancin Sin ba ya bisa kan ka'ida, kuma ba shi da ma’ana. 

Kaza lika jami’in ya ce bangaren Sin zai ci gaba da kare ikon mulkin kasar da hakkinta na teku. A sa’i daya kuma, zai dage wajen warware rikicin dake da nasaba da teku ta hanyar tattaunawa.

A gun taron tattaunawar Shangri-La karo na 21, shugaban Philippines Marcos ya gabatar da jawabi, inda ya sanar da cewa, yarjejeniyar dokokin tekun kasa da kasa ta MDD, da hukuncin shari’ar tekun kudancin Sin, dukkansu sun amince da hakkin Philippines bisa doka. (Safiyah Ma)