logo

HAUSA

Isra’ila na ci gaba da daukar matakan soja a Rafah

2024-06-03 11:16:57 CMG Hausa

Sojojin kasar Isra’ila sun ci gaba da aiwatar da matakan soja a zirin Gaza har zuwa jiya Lahadi 2 ga wata, inda a cewar kafafen yada labaran Palesdinu, sojojin Isra’ila suka kai harin sama, da harin boma-bomai kan yammacin birnin Rafah, da zirin Philadelphi, wato yankin dake kan iyakar kasar Masar da kudancin zirin Gaza.

A ranar 29 ga watan Mayu, majalisar dokokin Isra’ila ta amince da wani shirin doka, wanda ya ayyana hukumar UNRWA dake karkashin Majalisar Dinkin Duniya, a matsayin “kungiyar ’yan ta’adda”. Kaza lika, majalisar dokokin Isra’ila za ta kara jefa kuri’a kan wannan doka.

Irin wannan abun da Isra’ila ta yi, ya janyo babban suka daga hukumar UNRWA da MDD gami da sauran kasashen duniya, inda a cewarsu, babu wata kasa dake da ikon ayyana wata babbar hukumar MDD a matsayin “kungiyar ’yan ta’adda”, kuma hakan zai tsananta halin da ake ciki a yankin. (Murtala Zhang)