logo

HAUSA

Wakilin shugaba Xi ya halarci bikin shan rantsuwar shugaban El Salvador

2024-06-03 13:34:24 CMG Hausa

 

Bisa gayyatar da shugaban kasar El Salvador Nayib Bukele ya yi masa, wakilin musamman na shugaban kasar Sin, kuma ministan raya al’adu da yawon bude ido na kasar Sun Yeli, ya halarci bikin shan rantsuwar shugaban El Salvador a ranar Asabar 1 ga watan Yunin nan.

Mista Bukele ya kama aiki a matsayin shugaban El Salvador a sabon wa’adi, bayan rantsuwar da ya sha a birnin San Salvador, fadar mulkin kasar ta El Salvador. Yayin taron rantsuwar, shugaba Bukele ya yi takaitacciyar ganawa da Sun Yeli.

Sun Yeli ya gabatar da sakon shugaba Xi Jinping, na taya Bukele murna da fatan alheri, yana mai bayyana aniyar kasar Sin ta aiki tare da El Salvador, wajen karfafa manufofin bunkasa kasa bisa manyan tsare tsare, da yayatawa, da bunkasa ci gaban alaka mai zurfi dake tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare kuwa, Bukele ya bukaci Sun Yeli da ya gabatar da sakon sa na godiya da fatan alheri ga shugaba Xi Jinping. Ya ce bunkasa dangantaka da Sin muhimmin aiki ne da El Salvador ta sanya gaba, kuma bangaren El Salvador a shirye yake ya zurfafa hadin gwiwa na cimma moriyar juna tare da Sin, da daga matsayin ci gaban alakar su zuwa sabon mataki.  (Saminu Alhassan)